in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin 'yan majalisun kasashen LCBC na nuna damuwa kan kafewar tafkin Chadi
2014-02-02 16:10:53 cri
Shugabannin 'yan majalisun kasashe mambobin kwamitin tafkin Chadi (LCBC) sun nuna damuwarsu a kwanan nan kan kafewar da tafkin ke ci gaba da yi da illar da wannan matsala za ta janyo wa al'ummomi fiye da miliyan 30 dake rayuwa a yankunan dake gaba da Sahara.

Shugabannin 'yan majalisu daga Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi sun yi wata ganawa a birnin Abujan Najeriya a karkashin jagorancin shugaban majalisar wakilan Najeriya malam Aminu Waziri Tambuwal domin tattauna hanyoyin da za'a bi wajen warware wadannan matsalolin da tafkin ke fama da su da muraba'insa ya ragu fiye da fadin kilomita dubu 25 a shekarar 1964 zuwa fadin kilomita dubu daya da dari biyar a halin yanzu.

A gaban wannan matsala, kungiyar bunkasa noma da cimaka ta MDD da kimanta ragewar tafkin da bala'in muhalli, tare da jaddada cewa wannan zai janyo manyan matsaloli ga mutane miliyan 30 dake rayuwa a wannan shiyya.

Ganin cewa wadannan kasashe mambobin LCBC sun dauki niyyar kara dalar Amurka 14.6 domin sake raya tafkin Chadi, mista Tambuwal ya bayyana cewa 'yan majalisun kasashen da wannan matsala ta shafa za su yi aiki tare domin ceto tafkin Chadi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China