Bisa wannan shirin, gwamnatin kasar za ta samu kundin nuna hanya da zai taimaka wajen daidaita bangaren samar da iri a cikin wannan kasa.
Haka kuma za'a kafa wata dokar da ta shafi wannan fanni sannan a gabatar da ita ga majalisar dokoki, matakin da zai baiwa gwamnatin kasar damar samun tsarin kafa jadawalin ayyukan da za su taimaka bunkasuwar fannin samar da iri, in ji Moussa Mahamat Aggrey, ministan noma da ruwa na kasar Chadi.
Haka kuma ya bayyana cewa shirin za'a kafa shi ne tare da taimakon dukkan masu ruwa da tsaki na gwamnati, masu zaman kansu da kuma kungiyoyin manoma.
Akwai karancin amfani da iri ga manoman kasar Chadi, in ji Marc Abdallah, wani jami'in FAO dake kasar Chadi.
Kasar Chadi na da filayen noma, amma duk da wannan arziki da take da shi, al'ummominta musammun ma mazauna karkara na fama da matsalar karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki. (Maman Ada)