in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 229 sun mutu sanadiyar mahaukaciyar guguwa
2013-11-11 15:30:11 cri

Hukumar rage radadin bala'u ta kasar Philiphines ta sanar a yammacin jiya 10 ga wata cewa, ya zuwa karfe 7 na daren wannan rana agogon wurin, mahaukaciyar guguwar Haiyan, ta yi sanadin mutuwar mutane a kalla 229, yayin da wasu 45 suka jikkata, ban da haka, mutane 28 sun bace.

Hukumar kuwa ta bayyana cewa, adadin asarar rayuwa zai karu, har ila yau, ba a dawo da wutar lantarki da hanyoyin sadarwa ba tukuna duk da cewa ana kokarin maido da su.

Sakataren majalisar ministocin kasar Jose Aermendelasi ya furta cewa, yanzu an bude hanya zuwa wani birni inda aka fi fama da bala'in, inda jama'a ke matukar bukatar abinci da tantuna.

Bisa kididdigar baya-bayan nan da hukumar ta bayar, an ce, mahaukaciyar guguwar da ake kira "Haiyan" ta ratsa lardunan kasar 41, inda yawan mutane da suka yi asarar dukkiyarsu ya kai kimanin miliyan 9.5. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China