in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shelanta kashedi mafi girma a kusantowar guguwar Fitow
2013-10-05 20:52:11 cri

Hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar Sin ta shelanta kashedi mafi girma a ranar Asabar a kusantowar guguwar Fitow a yankunan gabar bakin teku dake kudu maso gabashin kasar.

Fitow zai iso a yankunan gabar teku tsakanin tsakiyar lardin Zhejiang da kuma arewacin lardin Fujian tsakanin ranar Lahadi da yamma da ranar Litinin da safe.

A cewar hukumar kula da hasashen yanayi ta kasar Sin (CMN), bisa cewa guguwar za ta zo yankunan bakin ruwa na kudu maso gabashin kasar Sin a cikin watan Oktoba abu ne da ba kasau ba ake gani, haka kuma ta gargadi hukumomi da mazauna wuraren da kara yin hattara da kuma sauraren labarai da suka shafi wannan batu.

Hukumar CMN ta yi hasashen cewa, Fitow za ta zo tare da iska mai karfin gaske zuwa ruwan teku na arewa maso gabashi da kuma arewacin tsibirin Taiwan, da kuma gabashin Zhejiang da Fujian nan da sa'o'i ishirin da hudu.

Kasar Sin ta tanadi tsarin yin kashedi ta fuskar hasashen yanayi na matsayin kaloli hudu, kalar ja na matsayin koli sannan ruwan goro, masara da shudi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China