Bisa rahoton da hukumar kula da harkokin cikin gida ta lardin Guangdong ta bayar, ya zuwa ranar 23 da karfe 8 na safe, mutane kimanin miliyan 3 da dubu 563 suka gamu da mahaukaciyar guguwar iska ta Tiantu, cikinsu mutane 25 sun rasu, kana kuma an kauratar da mutanen da yawansu ya kai dubu 226, sannan bala'in ya haddasa lalacewar gidaje 7100 da hasarar dukiyoyin na kimanin kudin Sin Yuan biliyan 3.24.
Ya zuwa yanzu, hukumar rage bala'i da hukumar kula da harkokin cikin gida ta lardin Guangdong sun kafa shirin ko ta kwana cikin gaggawa, don tura rukunin aiki zuwa yankunan da bala'in ya shafa, wajen taimaka wa jama'a da suka gamu da bala'in farfado da zaman rayuwarsu.(Bako)