in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da takwarar aikinsa ta kasar Argentina
2014-07-19 16:47:24 cri
Jiya Asabar 18 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwarar aikinsa ta kasar Argentina Cristina Fernandez de Kirchner a babban birnin kasar Argentina, Buenos Aires. A yayin ganawarsu, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyinsu game da harkokin da suka shafi dangantakar kasashen biyu da wasu batutuwan dake janyo hankulansu, inda suka cimma matsayi guda kan daga dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da amincewa da juna domin neman ci gaba cikin hadin gwiwa, karfafa hadin gwiwar kasashen biyu bisa moriyar juna ta yadda za a iyar tallafa wa jama'ar kasashen biyu yadda ya kamata, da kuma habaka hadin gwiwarmu tare da kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa da kuma kasashe masu tasowa.

Haka kuma, shugabannin biyu sun amince da kuma samar da wata hadaddiyar sanarwa ta kafuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasar Sin da kasar Argentina. Bugu da kari, shugabannin biyu sun halarci taron kullawar wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa dake tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da suka shafi harkokin tattalin arziki da zuba jari, canjin kudaden dake tsakanin kasashen biyu, gina kayayyakin more rayuwa, ayyukan noma, samar da wutar lantarki ta makamashin nukiliya da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China