Hukumar tsaro ta kasar Mali ta ce an hallaka mutane 8 daga cikin mutane 30, da dakarun azbinawa suke garkuwa da su a babban yankin Kidal da ke arewacin kasar Mali.
Rahotanni dai sun ce an hallaka mutanen ne a ranar 17 ga wata, wadanda 2 daga cikinsu fararen hula ne, yayin da kuma ragowar 6 ma'aikatan gwamnati ne, koda yake dai ba a sanar da cikakkun sunayensu ba.
Firaministan kasar mali Moussa Mara ya isa Kidal don ziyarar aiki a yammacin wannan rana ta Asabar 17 ga wata, a karon farko da ya ziyarci arewacin kasar, tun bayan darewarsa mukamin Firaminista a watan Afrilu.
Sanar da wannan ziyara ta sanya dakarun yankin na Kidal, dake goyon bayan kungiyar 'yan a ware ta MNLA a arewacin kasar bayyana adawa da hakan. Inda suka yi musanyar wuta da sojojin gwamnatin kasar. A kuma dai yammacin wannan rana, dakarun sun kai farmaki babban ginin gwamnatin yankin na Kidal, inda suka yi garkuwa da ma'aikatan gwamnati fiye da 30, wadanda suka kunshi wasu gwamnoni, da magajin gari, da ma'aikatan gwamnati da kuma wasu fararen hula.
Bisa sanarwar da ministan tsaron kasar ta Mali Soumeylou Boubeye Maiga ya bayar a ranar 18 ga wata, an ce, dauki-ba-dadin da aka yi a ranar 17 ga wata, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 36, tare da jikkata wasu karin mutane 87. (Danladi)