Bayanai na cewa, harin da 'yan tawayen suka kai kan sojojin ya haddasa mutuwar mutane 36, lamarin da ya saba wa yarjejeniyar Ouagadougou da aka sanya hannu a kai a watan Yunin shekarar 2013 tsakanin gwamnatin rikon kwaryar kasar da kungiyoyin 'yan tawayen.
Sai dai bayan dawowarsa birnin Bamako, firaministan ya bayyana cewa, yanzu kasar ta shiga yaki da 'yan tawayen na MNLA, inda ya bayar da umarnin tura karin dakaru zuwa yankin.
Ya ce, an dauki wannan mataki ne domin kawo karshen matsayin kawo sarki da garin ke fuskanta tun lokacin da 'yan tawayen suka fara tayar da kayar baya a watan Janairun shekarar 2012. (Ibrahim)