Kakakin shugaban kasar Afrika ta Kudu, Mac Maharaj, ya ce, Afrika ta Kudu za ta bunkasa cinikayyar da take yi da sauran kasashen mambobin kungiyar BRICS, kuma dama tuni kasar ta samu gagarumin ci gaba a huldar kasuwancin da take yi da sauran kasashen BRICS, wadanda suka hada da Brazil, Rasha, India, Sin.
Mac Maharaj ya kara da cewar, habbaka huldar cinikayya tsakanin kasashen BRICS, ya zamanto wata babbar manufar Afrika ta Kudu.
Tuni dai shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma, ya isa Fortaleza, dake Brazil, domin halartar taron koli, karo na shida, na kungiyar ta BRICS, mai taken "Kungiyar BRICS: samar da cikakken ci gaba mai dorewa."
Kakakin shugaban kasar ta Afrika ta Kudu, ya ce, kasancewar Afrika ta Kudu a cikin kungiyar BRICS, ya taimakawa kasar cimma muradunta, ta hanyar ba da fiffiko wajen aiwatar da manyan ayyuka na tattalin arziki, masu alaka da rage kaifin talauci, samar da ayyukan yi, da kuma dakusar da banbanci tsakanin jama'a.
A shekarar 2013, cinikayya tsakanin Afrika ta Kudu da kasashen dake cikin kungiyar BRICS, ta kai darajar dalar Amurka biliyan 36, kuma wannan adadi, ya nuna an samu karuwar cinikayya da kusan kashi 27.5 bisa dari idan aka kwatanta da adadin cinikayyar da aka yi a shekarar 2012, inda darajar cinikayyar ta kai dalar Amurka biliyan 28.
Maharaj ya kara da cewar, Afrika ta Kudu na da muradin bunkasa huldar cinikayya tsakanin BRICS da sauran kasashen Afrika. (Suwaiba)