in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
BRICS na shirin kafa sabon bankin samar da ci gaba
2014-07-16 09:45:57 cri

Shuwagabannin kungiyar kasashen da arzikinsu ke saurin bunkasa ta BRICS, sun bayyana aniyar kafa wani bankin musamman na tsimi da samar da ci gaba.

Kasashen Brazil, da Rasha, da India, da Sin da kuma Afirka ta Kudu, dake matsayin mambobin kungiyar ne suka fidda taswirar kafuwar bankin a jiya Talata, yayin taron BRICKS karo na 6 da suke gudanarwa a birnin Fortalezan kasar Brazil.

Wata sanarwa da aka fitar yayin taron ta nuna cewa, helkwatar sabon bankin na NDB za ta kasance ne a birnin Shanghai na kasar Sin, yayin da ake sa ran zuba masa jarin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu 100. A daya bangaren kuma za a bude ofishin shiyyar bankin ta Afirka a kasar Afirka ta Kudu.

Kaza lika sanarwar ta bayyana cewa, shirin kungiyar ta BRICKS na tsimi da aka yiwa lakabi da CRA, wanda zai fara aiki da jarin dalar Amurka miliyan dubu 100, zai baiwa kasashe mabukata damar kaucewa fadawa matsalolin kudi, da samar da rance domin rage kaifin matsalolin tattalin arziki. Har wa yau ana fatan wannan tsari zai taimaka wajen kara hada kan kasashe mambobin kungiyar ta BRICKS, tare da baiwa tsarin tattalin azikin duniya kariya ta musamman, bisa tsare-tsaren da ake da su a halin yanzu. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China