in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jaridar "People's Daily" ta kasar Sin ta yi sharhi cewa, ya kamata a kara hadin kai a tsakanin kabilun kasar Sin
2014-06-03 14:25:00 cri

A ranar 3 ga wata, Jaridar "People's Daily" ta kasar Sin ta yi sharhi cewa, ya kamata a kara hadin kai a tsakanin kabilun kasar Sin. Sharhin ya ce, tun fil aza, jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kasance wani yanki ne da kabilu da yawa ke zama. A yankunan da ke kudanci da kuma arewacin dutsen Tianshan na Xinjiang, mutane miliyan 22.6 daga cikin kabilu 47 suke zama tare a wannan wurin. Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a taron aiki kan Xinjiang cewa, batun da za a mai da hankali cikin dogon lokaci shi ne hadin kai a tsakanin kabilu daban daban a Xinjiang, hadin kai ya zama wani abu mai muhimmanci ga 'yan kabilu daban daban da ke zama a Xinjiang. Idan ana son tafiyar da harkokin Xinjiang yadda ya kamata, to, tilas ne a karfafa hadin kai a tsakanin kabilu daban daban a Xinjiang.

Sharhin ya ci gaba da cewa, hadin kai da zaman karko zai samar da alheri ga jama'a, jawo baraka zai kawo hadari ga jama'a. Bayan harin ta'addanci a birnin Kunming na kasar Sin, wani jami'i dan kabilar Uygur ya bayyana matsayin jama'ar kasar biliyan 1.3 cewar, yayin da masu jawo baraka suke kokarin lalata hadin kai a tsakanin kabilu daban daban, ya kamata mu kara inganta hadin kansu, don gina wata katanga mai karfi wajen tabbatar da zaman karko a zamantakewar al'ummar kasar Sin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China