Shugaba Xi Jinping ya bayyana hake ne a yayin taro na biyu na tattaunawa kan ayyukan gina jihar Xinjiang da aka yi a nan birnin Beijing daga ranar 28 zuwa ta 29 ga watan. Bugu da kari, shugaba Xi ya kara da cewa, manyan ayyukan kasar Sin wajen gina jihar Xinjiang su ne, tabbatar da zaman karko a jihar da kuma samun dauwammamen ci gaban jihar. Dole a mai da aikin yaki da aikace-aikacen ta'addanci da na tashin hankali a matsayin aiki mafi muhimmaci a halin yanzu, a sa'i daya kuma, a karfafa hadin gwiwa tare da kasashen duniya wajen yaki da ta'addanci. Game da haka, ya kamata a kara kokari bisa dogaro da karfin kabilu daban daban na kasar, da zurafafa mu'amalar dake tsakaninku, ta yadda za a samu unguwanni masu zaman lafiya dake kunshe da kabilu daban daban. (Maryam)