Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi wannan sanarwa a yayin taron kungiyar ECOWAS karo na 45 a birnin Accra na kasar Ghana.
Hakan ya biyo bayan kaddamar da gidauniya ta musammun a yayin wannan taro domin yaki da yaduwar kwayoyin cutar Ebola a shiyyar, wannan taimako ya cimma dalar Amurka miliyan 3,5 da Nijeriya ta baiwa Guinee, Sierra Leone, kungiyar kiwon lafiya ta yammacin Afrika (OOAS) da kuma asusun hadin gwiwa na ECOWAS kan yaki da cutar Ebola.
A Liberiya an samu mutane 87 da suka mutu daga cikin mutane 131 da suka kamu da cutar da aka tabbatar in ji mataimakin shugabar kasar Liberiya, Joseph Boakai a yayin taron.
A Liberiya, Guinee da Sierra Leone, kasashen da cutar Ebola ta fi tsanani ya zuwa yanzu an kiyasta mutane 844 suka kamu da cutar yayin da mutane 518 suka mutu a cewar darektan kungiyar OOAS, Xavier Crespin.
Ana bukatar kimanin dalar Amurka miliyan 15 domin yaki da cutar Ebola ganin yadda take kamari a cikin wadannan kasashe uku da kuma hana yaduwarta zuwa sauran kasashen yammacin Afrika in ji mista Crespin. (Maman Ada)