140708murtala.m4a
|
Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam, a lokacin kaddamar da sayar da takin zamani na daminar bana da aka yi a gidan gwamnatin jihar dake garin Damaturu.
Gwamna Gaidam ya kara da cewa, irin wannan hobbasa bai tsaya tsakanin gwamnatin jihar da karamar hukumar Fune kawai ba, domin kuwa a kwanakin baya ma, sun cimma irin wannan kuduri kan samar da ruwa da karamar hukumar Damaturu a kan kudi Naira miliyan 40, kuma wannan shiri zai karade kusan dukannin kananan hukumomin jihar 17 a nan gaba.
Gaidam ya kara da cewa gwamnatin jihar Yobe ta yanke shawarar gudanar da irin wadannan ayyukan raya kasa ne, domin sake habaka tattalin arzikin jihar, musamman ganin yadda Allah ya albarkaci jihar da kasar noma mai yalwa, tare da koguna da makwancin ruwa wadda kan iya taimakawa ta fuskar noman rani da na damina, kari kan kasancewar mafi yawan al'ummar jihar manoma ne.
Kamar yadda gwamnan ya ce, ganin cewar gwamnatin jihar ta dauki harkokin noma da matukar muhimmanci, ya sa a kasafin kudin bana ta ware zunzurutun kudi har Naira Miliyan 200, don ba da rancen sayo shanun noma ga manoma, don su samu saukin gudanar da sana'ar su, kuma tuni a kalla manoma dubu daya suka ci gajiyar wannan shiri a dukkanin fadin jihar ta Yobe.
Daga nan sai gwamnna Ibrahin Gaidam ya yi kira ga sarakuna iyayen kasa, da su ci gaba da umartar al'umma wajen ci gaba da addu'ar rokon ruwa, domin samun damina mai yalwa kana ya kuma nemi al'umma da su ci gaba da yin addu'ar samun dorewar zaman lafiya a jihar, da ma Najeriya baki daya. (Murtala Zhang)