Yau Laraba 9 ga wata ne aka bude taron tattaunawa a tsakanin kasashen Sin da Amurka kan fannonin manyan tsare-tsare da tattalin arziki karo na 6 da kuma shawarwari a tsakanin manyan jami'an kasashen 2 ta fuskar mu'amalar abubuwan da ke shafar rayuwar dan Adam na yau da kullum karo na 5 a nan Beijing, inda shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi jawabi mai lakabin "A yi kokarin kafa dangantaka ta sabon salo a tsakanin Sin da Amurka".
A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ce, yadda Sin da Amurka suka tabbatar da tunanin juna bisa manyan tsare-tsare zai yi babban tasiri kai tsaye kan manufofin da kasashen 2 za su dauka da kuma wace irin hulda za su kafa a tsakaninsu. Don haka bai kamata a yi kuskure a wannan fanni ba. In ba haka ba, za a yi kuskure baki daya. Ya kamata Sin da Amurka su kara yin tattaunawa a tsakanin juna, su inganta amincewar juna, da kyautata hadin gwiwar da ke tsakaninsu, a kokarin tabbatar da kafa dangantaka ta sabon salo a tsakanin kasashen 2.
Xi ya kara da cewa, Sin da Amurka, kasashe ne dake da halin musamman nasu. Akwai bambanci a tsakaninsu a fannoni daban daban, don haka suna bukatar tuntubar juna da hada kai. Ya kamata kasashen 2 su tsaya tsayin daka kan bin manufar kafa dangantaka ta sabon salo a tsakaninsu, su mai da hankali kan neman samun moriyar bai daya a maimakon sabanin da ke tsakaninsu. Har wa yau kamata ya yi su yi zaman daidai wa daida da kuma girmama juna a sassa daban daban, musamman ma ikon mulkin kasa da cikakken yankin kasa da hanyar da suka bi wajen raya kasa. Wajibi ne su daidaita matsala da sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata, su nace ga inganta amincewar juna da kara cimma ra'ayi daya ta hanyar yin tattaunawa da shawarwari.
Shugaban Sin ya ci gaba da cewa, a cikin sabon yanayi da ake ciki, ya kamata kasashen Sin da Amurka su karfafa hadin gwiwarsu da kuma habaka fannonin hadin gwiwarsu, ya dace da mu gaggauta shawarwarinmu kan harkokin zuba jari, don cimma wata yarjejeniyar da za ta dace da moriyar juna cikin sauri, wadda za ta kuma inganta dangantakar tattalin arzikin dake tsakanin kasashen biyu. Haka kuma, ya kamata a zurfafa shawarwarin dake tsakanin sojojin kasashen biyu, kyautata tsarin shawarwari da na hadin gwiwa, don ciyar da dangantakar sojojin kasashen biyu gaba, sa'an nan kuma, ya kamata mu hada kai wajen yaki da 'yan ta'adda. Bugu da kari, ya kamata mu dauki alhakin fuskantar kalubalen sauyin yanayi, karfafa shawarwari da mu'amalar dake tsakanimmu kan manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a iya ba da karin gudummawa wajen kiyaye da kuma inganta zaman lafiya da na karko a duniya baki daya. (Tasallah & Maryam)