in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Habasha
2014-07-10 09:23:59 cri

A jiya ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Habasha Mulatu Teshome a nan birnin Beijing, inda Xi Jinping ya bayyana cewa, an samu nasarori da dama yayin da aka inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma dangantakarsu ta zama abin koyi a Afirka har ma a kasashe masu tasowa na duniya.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar Habasha da ta samu wadata, kana tana son yin mu'amala kan harkokin siyasa tare da kasar Habasha, da kara hadin gwiwarsu a dukkan fannoni, da yin musayar fasahohi a tsakaninsu a fannonin zuba jari, kafa yankin ciniki na musamman da yankin masana'antu, da kuma kara hadin kansu a fannonin koyar da fasahohi da horar da kwararru da dai sauransu. Hakazalika kuma kasar Sin na da aniyar hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Habasha a bangaren harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A nasa bangare, shugaba Mulatu ya bayyana cewa, akwai zumunci a tsakanin kasarsa da kasar Sin. Gwamnatin kasar Habasha da jama'arta suna nuna godiya ga kasar Sin bisa ga goyon baya da gudummawar da take ba su. Kasar Habasha tana gaggauta bunkasa tattalin arzikinta, don haka tana son yin koyi da fasahohin Sin, da yin marhabi da zuwan kamfanonin Sin da su zuba jari a kasar, da kuma fadada hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a fannonin aikin gona, kere-kere, ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa da dai sauransu. Kana shugaban ya yi imanin cewa, tabbas ne hadin gwiwar dake tsakanin Habasha da Sin za ta bada gudummawa ga cigaban dangantakar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China