Kwamishinan ciniki, masana'antu da harkokin zuba jari na jihar Barrister Kemela Okara ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, taron zai samu halartar shugabannin 'yan kasuwa daga sassa daban-daban na duniya.
Okara ya ce, gwamnati na samar da yanayin da ya dace baya ga cikakken tsaro da kayayyakin more rayuwa ta yadda yankin zai iya janyo hankulan masu sha'awar zuba jari kamar Dubai.
Allah ya albarkaci jihar Bayelsa da gurbataccen mai da kuma gas. (Ibrahim)