Shugaba Bouteflika wanda ya bayyana hakan ya yin da ya taryi shugaban hukumar ta FAF, da kocin kasar Halilhodzic a ofishin sa, ya taya su murna, sakamakon abin da ya kira kata rawar gani da kulaf din kasar ya yi, kafin wasan su na karshe da kasar Jamus, wanda Jamus din ta lashe da ci 2 da 1.
A baya dai ana rade-radin mai yiwuwa ne koci Halilhodzic, ya sauya sheka zuwa wani kulaf din na daban, duba da yadda tun a watan Afirilun da ya gabata hukumar ta FAF ta bukaci ya sake sabunta kwantiragin sa, amma ya ce sai bayan gasar cin kofin na duniya.
Bugu da kari akwai batun kalamai dake nuna yiwuwar ya koma kulaf din Trabzonspor FC na Turkiyya.
Hakan dai na zuwa ne a gabar da shi kan sa shugaban hukumar ta FAF Raouraoua ke shaidawa 'makarraban sa, aniyar kammala batun wanda zai kasance mai horas da 'yan wasan kungiyar kasar, gabanin fara buga wasannin share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka, da za a yi a kasar Morocco tun daga watan Satumbar shekarar 2015 mai zuwa.
A hannu guda kuma akwai batun da ake yi cewa tuni Raouraoua ya nemowa kasar sabon koci, dan kasar Faransa mai suna Christian Gourcuff, wanda kuma shi ne mai horas da 'yan wasan Lorient FC a halin yanzu. Koda yake dai mai yiwuwa wannan batu ya gamu da cikas, sakamakon bukatar da shugaban kasar ta Aljeriya ya bayyana.
A ranar Labara ne dai tawagar 'yan wasan Aljeriyar ta isa gida, in da aka yi mata tarba ta musamman, kafin daga bisani shugaban Bouteflika ya gana da su, in da kuma ya bayyana mu su matukar gamsuwar sa da yadda suka taka leda a gasar ta bana. (Saminu Alhassan)