in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar 'yan wasan Jamus za ta yi bikin lashe kofin a mashigar Brandenburg
2014-07-11 10:01:07 cri

Hukumar kwallon kafa ta kasar Jamus (DFB) ta sanar da cewa, idan har 'yan wasanta suka lashe kofin na bana, to za su yi shagulgulan murnar lashe kofin tare da magoya bayansu a mashigar birnin Berlin ta Brandenburg.

Shugaban hukumar kwallon kafan kasar ta Jamus Wolfgang Nierbach, ya shaidawa manema labarai cewa, yin hakan nuna godiya ce ga goyon bayan da magoya bayan suka nuna wa tawagar kasar ta Jamus a yayin da suke kasar Brazil.

A hannu guda kuma, ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi bayani kan shagulgulan da za a yi yayin da za ta gana da 'yan wasan a Berlin idan har suka lashe kofin na duniya.

A ranar Lahadi ne kasar Jamus din za ta kara da Argentina a wasan karshe, kuma za su dawo gida ne ranar Talata 15 ga watan Yuli da safe. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China