Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) Sepp Blatter ya ce, guraben da ake kebe wa kasashen Afirka da Asiya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya sun kasa, idan aka yi la'akari da yawan kungiyoyin kwallon kafa da nahiyoyin ke da su a hukumomin kwallon kafan biyu.
Blatter ya bayyana hakan ne cikin sharhin da ya rubuta a mujallar da hukumar ta FIFA ke wallafa wa mako-mako, inda ya ce, akwai bukatar a duba yawan guraben da ake baiwa ko wace nahiya.
Shugaban na FIFA ya kuma yaba rawar da kasashen Afirka, arewaci da tsakiyar Amurka suka taka a gasar ta bana, inda a karon farko kasashe biyu daga nahiyar ta Afirka suka kai ga zagaye na biyu na gasar.
Bisa tsarin FIFA na yanzu, kasashen Afirka na da gurabe 5 ne yayin da nahiyar Turai ke da gurabe 13. (Ibrahim)