in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Argentina da doke Netherlands
2014-07-10 09:45:53 cri

Yanzu dai ta tabbata cewa, kasar Argentina ce za ta kara da Jamus a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da ke gudana yanzu haka a Brzail, bayan da Argentina ta yi nasara da ci 4 da 2 a bugun daga kai, sai mai tsaron gida a wasan da suka buga a jiya.

Kasashen biyu sun shafe mintoci 120 cur suna fafatawa, inda dukkan bangarorin biyu suka yi ta kaiwa juna munanan hare-hare. Ana kuma dab da kammala mituna 90 na wasan, sai da dan wasan kasar Netherlands Robben ya kusa jikawa Argentina lissafi, amma mai tsaron bayansu Javier Mascherano ya kange shi.

Sai dai duk da canje-canjen 'yan wasan da bangarorin biyu suka yi, hakan bai haifar da wani sakamakon ba, sai da aka kai ga karin lokaci bayan cikar mintuna 90 na wasan.

Kasar Argentina ta samu wannan nasara ce, bayan da mai tsaron gidanta ya kade kwallaye biyu da 'yan wasan Nertherlands suka buga. Yanzu ke nan Nerthelands za ta kara da Brazil ranar Asabar don neman gurbi na uku a gasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China