in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Argentina tana dab ta lashe kofin kwallon kafa na duniya, in ji Messi
2014-07-11 09:55:44 cri

Gwarzon 'dan kwallon kafan duniya kuma 'dan wasan kasar Argentina Lionel Messi ya ce, kasar tana dab da lashe kofin kwallon kafa na duniya na bana da ake fafata wa a kansa a kasar Brazil.

Messi ya yi wannan hasashe ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook, inda ya ce, sun sadaukar da nasarar da suka samu a wasan ranar Laraba da suka doke Netherlands da ci 4 da 2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida ga marubucin labaran wasannin nan 'dan kasar Argentina Topo Lopez da ya mutu sanadiyar hadarin mota a Sao Paulo a ranar da aka buga wannan wasa.

Yanzu dai Argentina za ta kara da Jamus ranar Lahadi a wasan karshe da za a yi a filin wasan na Maracana. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China