in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan bangarori daban daban su yi hakuri kan batun Ukraine
2014-06-16 19:08:25 cri
Bisa labarin da aka bayar an ce, a ran 14 ga wata, 'yan bindiga wadanda suke goyon bayan Rasha sun harbo wani jirgin dauken kaya na Ukraine a sararin saman birnin Luhansk, lamarin da ya haddasa mutuwar sojoji 49 wadanda suke cikin jirgin. Sannan a wancan rana, 'yan Ukraine wajen 300 sun kai farmaki kan ofishin jakandacin kasar Rasha dake kasar Ukraine.

Game da wadannan labarun, yau Litinin, a yayin wani taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana cewa, yanzu halin da ake ciki a kasar Ukraine yana jawo hankulan mutane sosai, ana fatan bangarorin da abin ya shafa su yi hakuri kan lamarin, kuma su hanzarta kawo karshen musayar wutar da ake yi a yankin domin magance mutuwar karin mutane, ta yadda za a iya kafa wani kyakkyawan yanayi ga kokarin daidaita batun Ukraine a siyasance. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China