in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 18 sun mutu yayin fada a Najeriya
2013-08-18 16:31:07 cri
Wasu kafofi da ma kafofin watsa labarai a kasar Najeriya sun bayyana cewa akalla mutane 18 sun rasa rayukansu a fada da aka yi a makon da ya wuce tsakanin dakarun gwamnati da 'yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Cikin matattun, guda 11 na daga cikin wadanda aka kashe ranar alhamis a wani sabon hari da ake kyautata zaton cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai a garin Damboa na jihar Borno dake yankin arewa maso gabashin kasar inji kafofi.

A kuma ranar juma'a, an kashe 'ya'yan kungiyar Boko Haram guda 7 yayin musayar wuta da 'yan sanda a jihar Gombe dake makwabtaka da ita inji kafofin watsa labaran kasar.

A Damboa, mazauna garin na zargin cewa wasu 'yan kasar waje masu magana da Larabci kuma masu farar fata suna daga cikin maharan.

Ayamu Lawal Gwasha, dan majalisa dake wakiltar Damboa a majalisar dokokin jihar Borno ya gayawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa har yanzu jama'arsa na zaman dar dar. (Lami Ali Mohammed)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China