Kakakin sojojin kasar Uganda ya ce wasu dakaru masu dauke da makamai su yi dauki ba dadi da sojojin gwamnati, bayan da suka yi yunkurin kaiwa wani sansanin sojojin da ke yammacin kasar hari a ranar Asabar 5 ga wata, lamarin da ya haddasa harbe maharan 41.
A zantawarsa da wakilin kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua ta wayar tarho, kakakin sojojin tsaron kasar Uganda Paddy Ankunda, ya ce tuni kura ta lafa, bayan da jami'an sojin kasar suka samu nasara kan dakarun da ke dauke da wukake, yayin da suke yunkurin aukawa sansanin sojojin a yammacin kasar.
Mr. Paddy ya kara da cewa, 'yan sandan kasar za su fara bin bahasin wadanda ke kitsa irin wadannan hare-hare ta bayan fage.
Shaidun gani da ido dai sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu, sakamakon aukuwar wannan hari. (Kande Gao)