Kungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF), ta bayyana damuwarta game da makomar wasu abokan aikinta su hudu da 'yan tawayen kasar Uganda suka kame.
Shugaban kungiyar ta MSF Mego Terzian, ya ce, akwai bukatar tabbatar da kare rayukan wadanda 'yan tawayen ke tsare da su, yayin da ake ci gaba da daukar matakan soji a yankin Beni, dake lardin Arewacin Kivu.
Terzian ya kara da cewa, duk da matukar kokarin da suka yi, sun gaza samun hakikanan bayanai, game da halin da tsararrun ke ciki. Duk kuwa da cewa sun tsananta bincikensu, a daidai gabar da ake tsaka da dauki ba dadi.
MSF ta bayyana cewa, akwai yiwuwar yawan wadanda 'yan tawayen ke tsare da su, su kai mutane 850.
Cikin watan Maris ne dai rundunar sojin yankin na Arewacin Kivu, ta samar da cewa, 'yan tawayen sun hallaka daukacin mutane 600 da suka tsare. (Saminu)