Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheik Muhamoud ya isa Kampala, babban birnin kasar Uganda a ranar Lahadi, inda zai yi shawarwari kan halin da kasarsa take ciki tare da takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni, in ji wata sanarwa ta fadar shugaban kasar Uganda ba tare da ba da wani karin haske ba.
Ziyarar shugaba Muhamoud ta zo a daidai lokacin da hare-haren mayakan kungiyar Al-Shabaab kan manyan mutanen siyasar kasar Somaliya ke karuwa.
Yau da wata guda, sojojin kasar Uganda fiye da 400, aka jibge a kasar Somaliya domin kare sansanoni da ma'aikatan MDD a wannan kasa dake fama da rashin tsaro. (Maman Ada)