Shugabar kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi bulaguro, jiya Laraba zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, domin halartar taron koli na yankin domin tattaunawa akan rikicin Sudan ta Kudu.
Wata sanarwa da ta fito daga fadar gwamnatin Uganda, ta bayyyana cewar, shugaban na Uganda Museveni, na halartar taron hukumar kasa da kasa na ci gaba, wanda ake sa ran zai kawar da matsalolin da ake fuskanta a shirin zaman lafiya da ake kokarin wanzarwa, tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da shugaban 'yan tawaye Riek Machar.
Kamar dai yadda sanarwa ta bayyana, taron wanda aka shirya za'a fara gudanar da shi a yau Alhamis, zai tattauna a kan cikakkun bayanai a game da rundunar samar da zaman lafiya da kariya wacce aka yanke shawarar turawa zuwa Sudan ta Kudu. (Suwaiba)