Rundunar 'yan sandan kasar Uganda ta yi gargadin cewa, mayakan Somaliya na shirin kai hari kan motocin dakon mai da ke yada zango da gidajen mai a kasar da ke gabashin Afirka.
Mataimakin kakakin 'yan sandan kasar Patrick Onyango ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, yana mai cewa, sun samu bayanan asiri da ke nuna cewa, akwai yiyuwar kai hari kan wuraren da motocin dakon mai ke yada zango kamar Naluwerere, Mbiko, Lugazi, Nakawa, Buwama, Lyantonde, Ruti, Rubaale, Karuma da kuma Elegu da ke kan iyaka da kasar Sudan ta Kudu.
Ya ce, sakamakon wannan lamari, rundunar ta dauki matakai ta hanyar tura jami'an tsaro da za su rika yiwa wadannan motoci rakiya da nufin shawo kan duk wata matsalar tsaro ba tare da bata lokaci ba.
Don haka, ya ce, suna kira ga dukkan dillalan mai da direbobin motocin daukar mai da su martaba matakan da aka dauka, baya ga kula da dukkan gidajen mai da difo-difon mai da ke fadin kasar baki daya.
Onyango ya kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su hada kai da jami'an yaki da ayyukan ta'addanci da kwamandojin da ke kula da yankunan kasar da wadannan motocin daukar mai ke ratsa wa ta cikin su, ta yadda haka za ta cimma ruwa. (Ibrahim)