in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uganda za ta tura karin dakaru zuwa CAR
2014-05-22 10:16:32 cri

Babban hafsan rundunar sojin kasar Uganda Janar Edward Katumba, ya ce, kasarsa ta shirin tura karin sojoji kasar Afirka ta Tsakiya CAR, domin shiga aikin wanzar da zaman lafiya karkashin tawagar MDD ta MINUSCA.

Da ma dai kasar ta Uganda na da dakarun soji sama da 4,000 a kasar Afirka ta Tsakiya, wadanda ke aiki cikin rundunar kasa da kasa, rundunar da ake fatan ta kunshi sojoji da yawansu zai kai 12,000.

Dakarun na Uganda na kuma taimakawa wajen fatattakar dakarun 'yan tawayen LRA, kungiyar da ya zuwa yanzu kotun hukunta manyan laifukan yaki ta kasa da kasa, ta ba da sammacin cafke jagoranta Joseph Kony, da wasu makarrabansa 4 bisa zargin su da aikata laifukan yaki.

Babban aikin rundunar MINUSCA dai shi ne baiwa fafaren hula kariya, tare da share fagen shigar da kayan agajin jin kai ga sassan kasar da yaki ya daidaita. Za ta maye gurbin rundunar MISCA dake karkashin kulawar kungiyar AU, tun daga ran 15 ga watan Satumbar dake tafe. Wa'adin aikinta zai kuma kare ne ranar 30 ga watan Afirilun shekarar 2015.

Kasar Afirta ta Tsakiya dai ta sha fama da rikice-rikice, tun daga watan Disambar shekarar 2012, lamarin da ya hallaka dubban jama'a, tare da raba sama da mutane 650,000 da gidajensu. Baya ga jefa kusan rabin al'ummar kasar da rikici ya yi cikin halin bukatar agajin jin kai. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China