Ko da yake a ranar Alhamis ne aka kai harin, sai a ranar Juma'a ne labarin ya isa kafofin watsa labarai ta bakin mazauna wajen, wani 'dan majalisa da jami'an tsaro. Mazauna garin suna zargin cewa wasu 'yan kasar waje, wadanda ke magana da harshen larabci kuma masu farar fata suna daga cikin wadanda suka kawo harin.
Mazauna garin sun kara da cewa, a kalla an gano gawawwaki 11 bayan harin.
Wani 'dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa a majalisar dokokin jihar Borno, Ayamu Lawan Gwasha ya bayyanawa wakilin kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa, har yanzu mutanen wajen suna zaman dar-dar.
Ya ce, sun nunawa mataimakin gwamnan jihar Borno, Zanna Umar Mustapha tsoro da suke ji, wanda kuma shi ma ya mika bayanin ga gwamnan jihar Kashim Shettima, kana an sanar da hukumomin tsaro. Ya ce yana ganin wannan mataki ya taimaka wajen rage munin harin.
Kokari da aka yi na jin ta bakin mai Magana da yawun rundunar tsaro ta hadin gwiwa (JTF), Lt-Col Sagir Musa ba ta cimma nasara ba, to amma wani babban jami'in soja ya tabbatarwa Xinhua da wannan hari.
Kafar sojin ta bayyana cewa daukar matakin gaggawa da dakarun tsaro suka yi ya sa masu harin sun gudu.(Lami Ali)