in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO ta bukaci a kara kokarin rigakafin annobar da ta shafi dabbobi
2013-04-06 16:59:01 cri
Dangane da yadda aka gano kwayoyin cutar murar tsuntsaye ta nau'in H7N9 a kwanakin baya, hukumar abinci da harkokin noma ta MDD, FAO a ranar 5 ga wata ta bukaci a kara kokarin rigakafin annobar da ta shafi dabbobi.

Babban likitan dabbobi na hukumar FAO, Mista Juan Lubroth, ya ce, tsaurara matakan rigakafin annobar da ta shafi dabbobi da na kiwon lafiyar dan Adam, zai taimaka a kokarin hana yaduwar annoba a tsakanin tsuntsaye ko kuma sauran dabbobi.

Mista Juan ya kara da cewa, sabanin kwayoyin cutar murar tsuntsaye mai nau'in H5N1 wacce ta haddasa mutuwar kaji da yawa a baya, wannan sabuwar kwayar cutar murar tsuntsaye mai nau'in H7N9 ba ta nuna alamun cutar cikin wasu 'yan kwanaki bayan da tsuntsaye suka kamu da murar, don haka yake da wuya a yi kashedi cikin lokaci, kuma su kansu manoma ba su san cutar na yaduwa tsakanin tsuntsayen da suke kiwo ba. Saboda haka, mataki mafi amfani shi ne, sanya manoma, makiyaya, ma'aikata masu harkar jigilar tsuntsaye da masu sayar da su a kasuwa, gami da sauran jama'a masu saye, su dauki matakan rigakafi, gami da na tsabtace muhalli.

Ban da haka, hukumar FAO ta kara da cewa, bayan da aka gano sabbin kwayoyin cuta mai nau'in H7N9, kasar Sin ta sanar da labarin kamuwa da cutar tsakanin jama'a cikin sauri, kuma nan take ta fara kokarin fadakar da jama'a dangane da kwayoyin cutar da yadda za a iya rigakafinta.

Bisa bayanai da gwamnatin kasar Sin ta samar, hukumar FAO da masu kimiyya da fasaha na kasashe daban daban suna kokarin nazari kan wannan kwayar cuta, da neman tabbatar da irin barnar da za ta iya haddasa ma sauran halittu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China