A wannan rana kafin ya kama hanya Xi Jinping ya fitar da bayani ta kafofin jaridun The Chosun Ilbo, JOONGAN DAILY da kuma Donga Daily na kasar Koriya ta Kudu, inda ya bayyana cewa, a cikin shekaru 22 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu, a karkashin kokarin su, ana samun nasarori masu yawa kan hadin gwiwar kasashen a dukkan fannoni.
Shugaba na Sin ya ce kasashen biyu sun kasance kasashe masu samun moriya iri daya, sannan kuma sun zama abin misali na raya dangantakar abokantaka a tsakaninsu a fadin duniya.
Mr. Xi Jinping ya lura cewa, a halin yanzu akwai damar samun babban ci gaba kan dangantakarsu, don haka yadda za a kara inganta dangantakarsu shi ne muhimmin batun da za a tattauna lokacin ziyarar da zai yi a kasar Koriya ta Kudu. (Zainab)