Wannan ne dai karon farko da shugaba Xi zai gudanar da ziyara a kasar Koriya ta Kudu, tun bayan da ya dare karagar shugabancin kasar Sin, lamarin da kuma ya sanya ziyarar tasa janyo hankalin kasashen duniya.
Kaza lika ziyarar ta shugaba Xi a wannan karo, ta biyo bayan wadda takwararsa ta Koriya ta Kudun Park Geun-hye ta gudanar bara a nan kasar Sin. An ce Xi Jinping zai yi shawarwari tare da shugaba Park Geun-hye, sa'an nan zai gana da shugaban majalisar dokokin kasar Chung Ui-hwa, da kuma firaministan kasar Chung Hongwon.
Bugu da kari Xi, zai gabatar da jawabi a jami'ar Seoul, kana zai halarci tarukan tattalin arziki da cinikayya.
Kasashen duniya da dama dai na fatan samun kyakkyawan sakamako don gane da ziyarar shugaba Xi a wannan karo, tare da maida hankali a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da cinikayya, da al'adu da dai sauransu. (Zainab)