in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liberia ta fara shirin kau da rashin nasarar da take samu a gasar AFCON
2014-05-20 15:01:04 cri
Kocin kulaf din kwallon kafar kasar Liberiya Thomas Kojo, ya bayyana kyakkyawan fatan sa, game da shirin da kulaf din da yake horaswa ke yi, na kawo karshen rashin nasarar da ya sha fuskanta, ta gaza samun damar taka rawar gani, a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Yau dai shekaru 13 ke nan, tun bayan da a karon karshe Laberiyan ta samu damar shiga a dama da ita, a gasar cin kofin na nahiyar Afirka, wanda ya gudana a kasar Mali. Kafin dai gasar ta shekarar 2002, Laberiya ta halarci gasar a shekarar 1996 a Afirka ta Kudu, inda aka cire ta a zagayen farko.

Sai dai a wannan karo a cewar kocin kungiyar wanda kuma ke cikin jerin 'yan wasan kasar na shekarar 2002, ya na fatan jagorantar 'yan wasan na sa, wajen karya matsayin rashin nasarar ta su. Kojo ya ce hakan babban buri ne ga 'yan wasan kasar Laberiya.

Game da dabarun da kocin ke ganin za su aiwatar domin cimma burin na su, Kojo na ganin za su yi kokarin baiwa ko wane wasa da za su buga kulawar da ta dace. Inda yanzu haka za su fara da wasan zagayen farko na neman tikitin gasar ta AFCON, a wasan da za su buga da kulaf din Likuena na kasar Lesotho a birnin Monrovia ranar Lahadi.

"'Yan wasan kasar Lesotho suna da kwarewa, don haka ba zamu yi wasa ba, na ji dadi kasancewar mu ne za mu karbi bakuncin wasan farko, burin mu shi ne samun nasara, ta yadda wasan mu na gaba a Maseru ba zai yi mana wuya ba" A kalaman kocin Laberiya Kojo.

Bugu da kari Kojo ya gayyato 'yan wasan dake buga wasannin a manyan kulaflikan waje, ciki hadda Sekou Jabateh wanda ke PAOK Salonika na kasar Girka, da Alseny Ocha-cha Keita dake wasa a Fransa, da dai sauran 'yan wasa da ake zaton za su iya tallafawa kulaf din, kaiwa ga nasarar da yake fata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China