Yobo wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan kammala wasan su da Faransa a filin wasan Mane Garrincha dake Brasilia, babban birnin kasar Brazil, inda kungiyar Faransa ta lashe Najeriya da ci 2 da nema, a ciki har da kwallon da Yobo ya ci gidansa guda daya a wannan wasan ana tsaka da zangon karin lokaci.
Dan wasan mai shekaru 33 a duniya dai ya dade yana taka kwallo a kulob din Fenerbahce na kasar Turkiya, a matsayin dan wasan baya, sai dai yanzu ya ce yana son mai da hankali ga iyalinsa, duk da sarkakiya dake tattare da wannan mataki da zai dauka.
A baya dai Yobo ya kasance cikin tawagar 'yan kwallon Najeriya a gasar cin kofin duniya har karo 3, ban da haka kuma ya jagoranci kungiyar Najeriya a matsayin kyaftin, inda ta lashe kambin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2013.
Duk da cewa dai Joseph Yobo ya kai ga kammala bugawa Super Eagles wasa a lokacin da suka hadu da rashin nasara, inda shi kan sa ya kasa taka rawar gani, a hannu guda bai yi da-na-sani ba. Ya ce shi da sauran 'yan wasan Najeriya sun samu damar shiga gasar cin kofin duniya, wanda a ganin sa wannan ma nasara ce, kuma sun riga sun taka rawar a-zo-a-gani a gasar dake da muhimmancin gaske. A cewarsa, bai ma zaci zai iya halartar gasar cin kofin duniya ta bana ba, ganin yadda ya kasa buga wasanni 6 da suka gudana a baya, a kakar wasanni ta bana sakamakon samun rauni da ya ji.
Sai dai duk da haka an ba shi wannan dama, don haka ya yi iyakacin kokari don taimakawa kungiyarsa samun cigaba a gasar, sai dai ba su yi sa'a ba a wannan karo.