Wannan ne dai karon farko da Ghana ta kasa kaiwa ga zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya a tarihin zuwan ta gasar, bayan da Portugal ta doke ta da ci 2 da 1 a wasan su na ranar Alhamis.
Da yake tsokaci game da hakan, shugaba Mahama ya ce akwai bukatar tantance musabbabin aukuwar wannan rashin nasara tun daga tushe, har ya zuwa lokacin buga wasannin da Ghanan ta kasa taka rawar gani a cikin su.
Daga nan sai shugaban na Ghana ya bukaci a yiwa kungiyar garan-bawul, yana mai baiwa al'ummar kasar hakuri kan abin da ya faru, tare da bukatar su da su ci gaba da baiwa kungiyar ta Black Stars goyon bayan da suka saba.
A bana dai kungiyar ta Ghana ta fuskanci tarin matsaloli, kama daga batun takaddamar kudade, da ta kusa kaiwa ga 'yan wasan kauracewa buga wasan su da Portugal, ya zuwa korar Sulley Ali Muntari, da Kevin-Prince Boateng, da mahukuntan kungiyar suka yi kafin wasan karshe.