Wani labari da majiya mai tushe ya nuna cewa, a yayin gasar kamfanoni fiye da 2300, daga kasashe 104 ne suka halarci kasar Brazil domin kallon gasar ta bana. Yayin da a kuma hannu guda suke shawarwari da wakilan gwamnatin kasar, da wakilan 'yan kasuwar kasar, musamman a fannonin harkar samar da kayan abinci, da aikin gona, da injiniyoyi, da harkar yawon shakatawa da dai sauransu. Matakin da ake fatan zai kara baiwa kasar damar samun karin jari da za a zuba ma ta, da karin damar fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a watanni 12 masu zuwa.
An ce muhimman kamfanonin da za su yi hadin gwiwa da kasar ta Brazil su hada da na Sin, da Amurka, da Japan, da na kasashen Turai da kuma kasashen nahiyar Latin Amurka.
Gasar cin kofin duniyar dai ta zama muhimman dandali mai fa'ida wajen kafa dangantakar hadin gwiwar cinikayya a tsakanin kasar ta Brazil da kuma sauran kasashen duniya.(Zainab)