Kocin na Super Eagles mai shekaru 52 da haihuwa, wanda ya taba taka ma kungiyar kwallon kafan Najeriyar kwallo a matsayin dan wasan baya, ya sanar da kudurin da ya tsayar na komawa gida don fuskantar sabbin kalobaloli, bayan da kungiyar Faransa ta lashe kungiyarsa da ci 2 da nema.
Keshi dai ya fara horar da 'yan wasan kungiyar Najeriya ne a shekarar 2011, inda ya jagoranci kungiyar wajen lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka. Kaza lika shi da Mahmoud El-Gohary dan kasar Masar ne kadai suka kasance mutane 2, kacal a nihiyar Afirka, da suka taba lashe kambin wannan gasa ta cin kofin Afirka a matsayin kociya, bayan sun daga kofin a matsayin 'yan wasan kungiyar su.
A lokacin ya na taka leda, Stephen Keshi ya ci ma kungiyar Najeriya kwallaye 64, tsakanin shekarar 1981 zuwa ta 1995, haka kuma ya taimakawa kungiyar samun nasarar daukar kofin nahiya Afirka a shekarar 1994 a kasar Tunisia.