in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Da dama daga 'yan kasar Brazil sun yi watsi da adawa ga gasar cin kofin duniya
2014-06-20 15:43:14 cri
Wasu bayanai daga biranen kasar Brazil dake daukar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a bana, na nuna cewa yayin da aka bude wannan gasa da dama daga al'ummar kasar Brazil sun yi watsi da batun adawar da ake zaton za su nuna ga gudanar ta, a maimakon haka 'yan kallo daga kasashen duniya daban daban, da na al'ummar kasar sun rungumi harshe daya na masu goyon bayan wasannin da ake bugawa.

Tun daga safiya zuwa dare, musamman a bakin teku dake birnin Rio de Janeiro, 'yan kallo daga kasashen duniya daban daban na gudanar da raye-raye da wake-wake cikin farin ciki a ko ina. Yayin da suma 'yan kasar Brazil din ke nuna farin cikin su yayin wasannin da ake bugawa. Wata 'yar kasar Brazil ta bayyana cewa, ta yi farin ciki kwarai da halartar mutane daga kasashe daban daban.

Duk dai da wannan tagomashi da gasar ke samu, da yammacin ranar Asabar 14 ga wata, yayin da kungiyar Uruguay ke wasa da Costa Rica a filin wasa na Kast Ron dake birnin Fortaleza na kasar ta Brazil, wasu gungun jama'a sun gudanar da zanga-zanga a daf da filin wasan, domin nuna adawa ga gasar cin kofin na duniya. Koda yake dai an ce yawancin al'ummar kasar sun fi maida hankali kan wasan, don haka masu zanga-zangar ba su da yawa. Kuma ba a dauki wani lokaci mai yawa ana gudanar da zanga-zangar ba.

Wani mutum dake birnin Fortaleza ya bayyana cewa, an yi zanga-zanga sau daya a birnin, amma ba ta yi wani tasiri ba, inda kimanin mutane 150 suka taru a daf da filin wasan na Kast Ron. An kuma hana su shiga filin wasan. A ganinsa, karancin masu zanga-zangar ya sa ba ta yi wani tasiri ba.

A dama daga jama'ar kasar ta Brazil dai na ganin cewa, gwamnatin kasar ta kashe kudade masu dama wajen gudanar da gasar ta cin kofin duniya, kuma koda yake ba su ji dadin hakan ba, a sa'i daya sai gasar za ta samarwa kasar babbar moriya. Wani direban mitar haya ya bayyana cewa, yanzu lokaci ne na gasar cin kofin duniya. An riga an kashe kudade masu yawa, kuma an fara gasar kai tsaye. Kungiyoyin kasashe daban daban da suka hallara a kasar ta Brazil don buga gasar ba su da wata alaka da siyasa, don haka kamata ya yi ayi maraba da su tare da nishadantar da su.

Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Brazil dai ta halarci dukkan wasannin wannan gasa 19 da aka buga, kuma a yanzu a iya cewa kwallon kafa ya sauya daga wasan tsaffin hannu zuwa na jama'ar duniya baki daya karni na 19 a wannan kasa. Ban da karin nuna sha'awa ga wasan kwallon kafa, 'yan kasar ta Brazil su na kara nuna sha'awar su ga batun sada zumunta da abokai da baki daga sauran kasashe ta hanyar wasan nan kallon kafa.

A hakika dai da fari an nuna shakku game da ikon gwamnatin kasar ta Brazil wajen gudanar da gasar cin kofin na duniya yadda ya kamata, amma yanzu an riga an fara wannan gasa. Don haka babu abin yi sai more nishadin dake kunshe ciki wasannin na wannan karo.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China