A cikin jawabinsa, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, kamata ya yi kasashen duniya su tabbatar da shirin bunkasuwa bayan shekarar 2015 bisa wata sabuwar hanya da kuma yin kwaskwarima. Haka kuma, kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya su yi la'akari da kiyaye muhalli yayin da suke tsara manufofinsu. A lokacin da shirin samun bunkasuwa na sabon karni na MDD ke dab da karewa, wato a shekarar 2015, kamata ya yi kasa da kasa su kafa sabon shirin samun bunkasuwa na bayan shekarar 2015.
An ci gaba da taron ministoci bayan rufe wannan taron, inda aka cimma matsaya kan sakamakon taron ministoci. Ministan kiyaye muhalli na Sin, Zhou Shengxian ya bayyana matsayin kasar Sin a yayin taron, inda ya ce, a fannin kiyaye muhalli da samun dauwamammen ci gaba, ana fatan kasashe masu sukuni za su kasance abin koyi, su canza hanyar tsarin samarwa da kayayyaki da amfanawa amfani da su da ba tai dace ba. Da Ministan kasar Sin shi ma ya nuna fatansa na ganin kasashe masu sukuni za su ba da taimako ga kasashe masu tasowa a fannonin fasaha, kudi, da dai sauransu.(Fatima)