Gurbacewar muhalli za ta iyar kasancewa dalilin janyo mutuwar mutane kimanin miliyan 3,7 a ko wace shekara a duniya, ta hanyar shakar sinadarai da sauran kananan abubuwan dake gurbata iska, in ji wani jami'in hukumar MDD kan muhalli UNEP.
Bisa kididdigar da aka yi, mutanen dubu dari shida da suka mutu, za'a iyar cewa, yana da nasaba da gurbacewar iska a cikin birane, yawancinsu na da nasaba da gurbacewar iska, in ji madam Jane Akumu, shugabar reshen tsare-tsaren hukumar UNEP dake mai da hankali kan kimiyya, masana'antu da tattalin arziki a yayin babban taron MDD kan muhalli a birnin Nairobi na kasar Kenya. Asarar da gurbacewar iska a cikin biranen Afrika za ta iyar kai zuwa kashi 2,7 cikin 100 na GDP, in ji madam Akumu.
Wani binciken baya bayan nan da jami'ar Nairobi ta gudanar kan asarar tattalin arzikin da aka samu, dalilin hayakin da motoci da sauran ababen hawa suke fitarwa da aka kiyasta ta kai dalar Amurka biliyan 1,3 a ko wace shekara. (Maman Ada)