Nahiyar Afrika na kusantowa da cimma matsayin tattalin arziki maras gurbata muhalli, fiye da sauran nahiyoyi, domin nahiyar ta fi kusa da muhallin halittu, in ji hukumar MDD kan muhalli (UNEP).
Babban darektan reshen tattalin arziki da kasuwanci na UNEP, mista Steven Stone, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a birnin Nairobi na kasar Kenya cewa, nahiyar Afrika na bukatar jari mai tarin yawa a cikin masana'antun da aka amfani da man fetur, kwal da sauransu.
Ko da wannan lokaci da ake samun bunkasuwa, bai kamata Afrika ta rasa wannan hanya ba, in ji mista Stone a yayin babban taron MDD kan muhalli a Nairobi. (Maman Ada)