in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya yi tsokaci game da ziyarar Barack Obama a Asiya da yankin tekun Pasifik
2014-04-30 20:45:19 cri
A yau Laraba 30 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Qin Gang ya yi magana game da ziyarar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi a wasu kasashen dake nahiyar Asiya da yakin tekun Pasifik, inda ya ce, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi bangarori daban daban da abin ya shafa su yi kokari tare domin kara amincewa da juna da sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da annashuwa a shiyya-shiyya. Kamata ya yi a tabbatar da zaman lafiya a yankin tekun Pasifik.

Dadin dadawa, Qin Gang ya kara da cewa, Sin na da iko game da bukatar yarjejeniyar da Amurka da Philippines suka daddale ta yadda za ta dace da wannan ka'ida, wato tabbatar da cewa yarjejeniyar ba za ta kawo illa ga amincewa da juna tsakanin kasashen dake wannan yanki da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki ba.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China