Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ga manema labaru yayin ziyarar da ya gudanar a kasar ta Kenya, ya ce MDD na goyon bayan kasar, za kuma ta taimakawa hukumomin tsaron ta a fagen karfafa kwarewarsu.
Har ila yau Mr. Ban ya ce ya samu damar tattaunawa mai ma'ana da daukacin bangarori masu ruwa da tsaki, game da al'amura masu alaka da siyasa da tsaro, da suka hada da yaki da ta'addanci, da yanayin da kasar Somaliya ke ciki, da batun kasar Sudan ta Kudu, da kuma na kasashen dake yankin manyan tafkunan Afirka.
Daga nan sai ya yi fatan mahukuntan kasar Kenya za su kai ga cimma babbar nasara, a kokarinsu na wanzar da zaman lafiya da lumana tare da kyautatuwar yanayin tsaro.
Kasar Kenya dai na fuskantar kalubalen hare-haren ta'addanci, musamman ma a sassan arewa maso gabashin kasar da kuma birnin Mombasa dake bakin teku. A daidai gabar da kuma dakarun take ci gaba da dauki ba dadi, da mayakan kungiyar Al-Shabab mai sansani a kudancin kasar Somaliya. Karkashin shirin wanzar da zaman lafiya da tawagar MDD ta AMISOM ke jagoranta. (Saminu Alhassan)