Kasar Kenya ta jaddada a ranar Laraba cewa, ba za ta janye sojojinta dake Somaliya ba, duk da karuwar hare-haren ta'addancin mayakan kungiyar Al-Shabaab na wannan kasa dake kusurwar Afrika.
Mataimakin shugaban kasar Kenya, mista William Ruto ya bayyana cewa, karuwar haren-haren ta'addanci ba zai tilastawa kasar Kenya ja da baya ba, sai dai ta ci gaba da rike nauyin dake bisa wuyanta a matsayin makwabciyar kasa, domin taimakawa ga tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya.
Kenya ba za ta gudu gaban nauyinta na makwabciyar kasa ba, za mu ci gaba da tsayawa cikin tsarin yarjejeniyar AMISON, har sai lokacin da aka cimma zaman lafiya a Somaliya, in ji mista Ruto a yayin wani taron manema labarai cikin hadin gwiwa tare da faraministan kasar Somaliya Abidweli Sheikh Ahmed, wanda ke ziyarar aiki a birnin Nairobi na kasar Kenya. (Maman Ada)