in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 4 sun rasu sakamakon harin da Al-Shabaab ta kaddamar a Kenya
2014-06-16 09:59:39 cri

A kalla mutane 4 ne aka tabbatar sun rasa rayukansu, baya ga wasu da dama da suka jikkata, yayin wani farmaki da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka kaddamar a kasar Kenya.

'Yan sandan yankin Lamu sun ce, maharan sun kone wasu otel-otel da wani aji-ofis a garin Mpeketoni dake bakin teku a daren jiya Lahadi. Lamarin da ya sabbaba rasuwar fararen hula 4.

Shaidun gani da ido dai sun ce, sun ga gawawwakin mutanen da harin ya ritsa da su, yayin da da dama da al'ummun yankin ke kokarin tserewa domin kaucewa musayar wutar da ta biyo bayan harin, tsakanin 'yan sanda da dakarun kungiyar ta Al-Shabaab su kimanin 20. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China