Kungiyar islama ta Al-Shabaab ta yi shelar cewa, ita ce ta kai mumunan har a garin Mpeketoni, wanda ke gabar ruwan kasar Kenya, harin da ta kai ya haddasa mutuwar kusan mutane 48.
Wata kafar yada labarai ta internet ta bayyana cewar, fiye da 'yan bindiga 50 ne suka kai hari a mashaya da wuraren shan kofi a yayin da mutane ke kallon kwallon kafa na duniya.
Wani shafin internet na Somalimemo ya ba da rahoto cewar, wata kungiya mai tsattsauran ra'ayi ta ce, ta kai harin ne a matsayin fansa, a kan musulman da ta yi ikirarin jami'an tsaron Kenya sun kashe a Mombasa.
An ba da rahoto cewar, kungiyar ta gargadi Kenya da ta janye dakarunta wadanda ke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a karkashin sojojin kiyaye zaman lafiya na tawagar kungiyar tarayyar Afrika AU da ke kasar Somaliya AMISON.
Kasar Kenya a yanzu haka sojojinta na kudancin Somaliya, inda suka taimaka suka tunkude gwamnatin 'yan tawaye daga kan mulki.
Ita kuma kungiyar islama ta Al-Shabaab tana adawa da kasancewar sojojin ketare a Somaliya, a inda kungiyar ta yi alkawarin daukar fansa a kan kasashen Afrika da suka tura sojojinsu zuwa ayyukan kiyaye zaman lafiya a Somaliya. (Suwaiba)