Mahukunta a kasar Kenya sun yi watsi da rade-radin da ake yi cewa, dangantakar kasar da kasashen yammacin Turai ta raunana, sakamakon kalubalen tsaro da a yanzu haka ke addabar kasar.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta nuna cewa, Kenya za ta ci gaba da aiki tare da daukacin abokan hadin gwiwarta a fannin inganta tsaro. Kuma hasashen da ake yi na yiwuwar samun koma baya ba shi da tushe bare makama.
Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka Nairobin Kenya ya shiga rukunin birane irin su New York, da Vienna da Geneva dake da damar karbar bakuncin babban taron MDD, kuma Kenya ita ce kasa daya tilo dake da wannan alfarma a kasashen da ke yankin kudancin duniya.
Wannan sanarwa na zuwa ne daidai gabar da wasu daga kafafen watsa labarun kasar ke hasashen cewa, sassa da dama, ciki hadda na tattalin arzikin kasar na iya samun koma baya, biyowa bayan matsalolin tsaro da ake fuskanta. Baya ga bangarorin dake baiwa kasar tallafi da ake ganin na iya rage huldar su da kasar. (Saminu)