in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya ba da umurnin kawar da miyagun kwayoyi
2014-06-25 20:11:52 cri
Ranar 26 ga wata, rana ce ta yaki da miyagun kwayoyi ta duniya. Domin wannan rana ta musamman, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurnin yaki da miyagun kwayoyi a kasar, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi gwamnatoci da kwamitocin JKS a matakai daban-daban su fahimci babban hadarin miyagun kwayoyi da muhimmancin yakar su, nauyi ne a kansu su dauki kwararran matakai domin gudanar da ayyukan yaki da miyagun kwayoyi cikin dogon lokaci.

Dadin dadawa, shugaba Xi ya bayyana cewa, aikin yaki da miyagun kwayoyi na da muhimmanci kwarai wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kawo alheri ga jama'a. A cikin 'yan shekarun da suka wuce, hukumomi a wurare daban daban sun aiwatar da manufofin yaki da miyagun kwayoyi da kwamitin tsakiyar JKS ya gabatar,inda suka yi gwagwarmaya tare da cimma babbar nasara. Kawo yanzu dai, ana ci gaba da fuskantar babban kalubale wajen yaki da miyagun kwayoyi a Sin, shi ya sa dole ne a ci gaba da yin kokari don ganin an kawar da wannan matsala.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China